Gov. Muhammad Badaru Abubakar on a Project Inspection Tour in some schools in Dutse LGA



In continuation of his inspection tour, the Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has yesterday visited some schools in Dutse LGA.
The Schools visited today are:

1. Fagoji Special Primary School, Dutse
2. Government Day Junior Secondary School Fagoji, Dutse
3. Government Girls Arabic Secondary School, Baure, Dutse

During the visits, Governor Badaru as usual visited classrooms to interact with the students and check the students and teachers registers, where he directed the State Ministry of Education and SUBEB to respond to all the challenges addressed immediately.

He also called on the teachers to give the students quality education right from the grassroot because of its enormous importance, where and also promised to give the much needed attention to education and teachers' welfare as at when due.

A cigaba da zagayen da yake yi na duba makarantu da ayyuka, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ma ya kai ziyarar wasu makarantu dake Ƙaramar Hukumar Dutse

Makarantun da Maigirma Gwamnan ya ziyarta yau sun haɗa da:

1. Makarantar Firamare na Musamman dake Fagoji, Dutse
2. Ƙaramar Sakandiren Gwamnati na jeka ka dawo dake Fagoji, Dutse
3. Makarantar Ƴan mata na Gwamnati na Koyon Larabci dake Baure, Dutse

A yayin ziyarar, Gwamna Badaru kamar yadda ya saba ya shiga azuzuwa domin ganawa da Ɗalibai, duba rajistar malamai da Ɗaliban, inda ya bada umarni ga Ma'aikatar Ilimi da Hukumar SUBEB su magance matsalolin da makarantun ke fuskanta.

Maigirma Gwamnan ya kuma yi kira ga malaman da su tabbatar sun bada ingantaccen ilimi tun daga matakin farko saboda muhimmancin sa, inda ya kuma yi alƙawarin bawa ɓangaren ilimin kulawa da baiwa malamai haƙƙoƙin su a sanda ya kamata.